الجمعة، رجب ٢٠، ١٤٣١

Gudunmwa AKramakAllah. FW: Muhimman Labarai Daga Muryar Amurka

Manyan Labarai

An Cire Najeriya

Duk da kunnen-dokin da Najeriya ta yi, an cire 'yan wasan Super eagles daga gasar cin kofin duniya ta 2010

Wani mai goyon bayan Super Eagles

An Fitar Da Afirka Ta Kudu Daga Gasar Cin Kofin Duniya

Duk da cewa ta doke Faransa a wasanta na karshe, Afirka ta Kudu ta zamo kasa mai daukar nauyin gasa ta farko da aka taba cirewa.

Wani dan Afirka ta Kudu yana share hawaye a karshen wasan kasar da Faransa yau talata 22 Yuni 2010 a Bloemfontein.

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Akalla 30 A Ghana

Hukumomin Ghana sun bayyana wannan ambaliya a Accra da tsakiyar Ghana a zaman mafi muni da aka gani cikin 'yan shekarun nan a kasar

Mata su na ficewa daga gidajensu a bayan da ambaliyar ruwa ta malale su a Accra, babban birnin Ghana

An Gano Jirgin Da Ya Fadi A Kamaru Dauke Da 'Yan Australiya

Gwamnatin Kamaru ta ce an gano garwar jirgin saman da ya bace dauke da manyan 'yan kasuwa na kasar Australiya su 11

Paul Biya

An Farfado Da Wani Shirin Rushe Gidajen Falasdinawa A Birnin Qudus

Hukumomin birnin Qudus sun farfado da shirin gina wurin shakatawa a wani wurin da za a rushe gidajen da Falasdinawa suka gina.

Benjamin Netanyahu

Kotun ECOWAS Ta Ce A Oktoba Zata Yanke Hukumci Kan Karar Hissene Habre

Kotun zata yanke hukumci a kan ko Senegal tana da hurumin gurfanar da tsohon shugaban na Chadi gaban kotu kan cin zarafin bil Adama

Tsohon hoto na Hissene Habre da aka dauka ranar 21 Oktoba, 1989 lokacin da ya kai ziyara Paris a Faransa, lokacin yana shugabancin kasar Chadi.

Switzerland Ta Doke Zakarun Turai, Spain

Zakarun Turai kuma kasar da wasu ke tsammanin zasu lashe kofin duniya a bana, Spain, sun sha duka a hannun 'yan wasan Switzerland

Honduras Ta Sha Kashi A Hannun Chile

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 48 da kasar Chile ta ke samun nasara a wata gasa ta cin kofin kwallon kafar duniya.

Kungiyar Red Cross Ta Ce An Kashe Daruruwa A Rikicin Kyrgyzstan

Shugabar Kyrgyzstan, Rosa Otunabyeva, ta furta cewa watakila adadin wadanda aka kashe ya zarce 176 da hukumomi suka bayyana

Didier Drogba Yace Sai 'Yan Sa'o'i Kafin Wasa Zai Yanke Shawara Kan Ko Zai Buga

Kyaftin din na 'yan wasan Ivory Coast yace talata ana dab da wasa zai ga ko kariyar da yayi a hannu zata kyale shi ya buga ma kasarsa

Karin Labarai

A cikin Wannan Email Din:

Labarai
Najeriya
Afirka
Sauran Duniya
Kiwon Lafiya

Cire Sunanka/ki

Idan an gaji da samun Kanun Labaranmu ta Email, to ana iya cire suna ko adireshi a nan Cire Sunanka/ki

Ana Bukatar Taimako?

Idan ana da wata tambaya game da Kanun Labaran nan, ana iya aika sako ga: Sashenhausa@VOANews.com

Mun sake tsarin dandalinmu domin ku samu saukin gano labarai, rahotanni, shirye-shirye, ko kuma sauti da bidiyo da hotunan da kuke bukata. Kuna iya aiko mana da ra'ayoyinku kan wannan sabon tsari namu zuwa ga: sashen-hausa@voanews.com

Cire Sunanka/ki


ليست هناك تعليقات: