الاثنين، ذو الحجة ١٦، ١٤٣١

Jumu'a babbar rana a Sunnar Baban fatima (AAYTGS),

Jumu'a babbar rana a Sunnar Baban fatima (AAYTGS), sai dai hankalin wasu bai yarda da wannan ba, tunanin su ya gano ranar da tafi daraja fiye da wacce Baki Me Albarka Ya ambata, har kuma suna ganin wanda bai yarda da hakan ba wai a gun su ya zama batacce ko ma suce bai son Annabi (TDAASTGS) Wannan danyan hukumci na kiran wanda bai ba da hadin kai a murguda hukunci ba da wani suna muna addu'ar Allah Ya kawo sauki da sauyi na gaskiya.
Abdu Bello Rishi.
Toro L.G.A.
Bauchi state
Ya Allah mu makafi ne Kai kuwa AlBaseeru, mu jahilai ne Kai kuma Al'Aleemu, mu na tawassuli da i'itirafin makantar mu, jahilcin mu da ajizancin mu, da kuma Ilmomin Ka, Hikmomin Ka da Qudrar Ka, Ka mana Jagora cikin dukkan abin da ya shiga mana duhu ko ya gagare mu, Ka bamu dace, da dacewa da kyakkyawan karshe, Ka tsarshe mu tabewa.
Abdu Bello Rishi. Mai gishirin zamzam S/naka.

ليست هناك تعليقات: