الأربعاء، رجب ١١، ١٤٣١

FW: Muhimman Labarai Daga Muryar Amurka

Manyan Labarai

An Gano Jirgin Da Ya Fadi A Kamaru Dauke Da 'Yan Australiya

Gwamnatin Kamaru ta ce an gano garwar jirgin saman da ya bace dauke da manyan 'yan kasuwa na kasar Australiya su 11

Paul Biya

An Farfado Da Wani Shirin Rushe Gidajen Falasdinawa A Birnin Qudus

Hukumomin birnin Qudus sun farfado da shirin gina wurin shakatawa a wani wurin da za a rushe gidajen da Falasdinawa suka gina.

Benjamin Netanyahu

Kotun ECOWAS Ta Ce A Oktoba Zata Yanke Hukumci Kan Karar Hissene Habre

Kotun zata yanke hukumci a kan ko Senegal tana da hurumin gurfanar da tsohon shugaban na Chadi gaban kotu kan cin zarafin bil Adama

Tsohon hoto na Hissene Habre da aka dauka ranar 21 Oktoba, 1989 lokacin da ya kai ziyara Paris a Faransa, lokacin yana shugabancin kasar Chadi.

Switzerland Ta Doke Zakarun Turai, Spain

Zakarun Turai kuma kasar da wasu ke tsammanin zasu lashe kofin duniya a bana, Spain, sun sha duka a hannun 'yan wasan Switzerland

Honduras Ta Sha Kashi A Hannun Chile

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 48 da kasar Chile ta ke samun nasara a wata gasa ta cin kofin kwallon kafar duniya.

Kungiyar Red Cross Ta Ce An Kashe Daruruwa A Rikicin Kyrgyzstan

Shugabar Kyrgyzstan, Rosa Otunabyeva, ta furta cewa watakila adadin wadanda aka kashe ya zarce 176 da hukumomi suka bayyana

Didier Drogba Yace Sai 'Yan Sa'o'i Kafin Wasa Zai Yanke Shawara Kan Ko Zai Buga

Kyaftin din na 'yan wasan Ivory Coast yace talata ana dab da wasa zai ga ko kariyar da yayi a hannu zata kyale shi ya buga ma kasarsa

Za A Kyale 'Yan Kallo Su Ci Gaba Da Busa Algaitar Roba

Masu shirya Gasar Cin Kofin Duniya a Afirka ta Kudu sun ce ba zasu haramta algaitar robar nan da ake kira Vuvuzela ba.

Vuvuzelas

Har Yanzu Ana Gwabza Rikicin Kabilanci A Kyrgyzstan

Jami'ai sun ce an kashe mutane 124, wasu har 1600 kuma suka ji rauni a wannan rikicin kabilanci da aka fara ran alhamis

Wani dan kabilar Uzbek ya rike kai yana kuka a kofar gidansa da aka kona kurmus a birnin Osh, litinin 14 Yuni 2010.

Arfirka Ta Kudu Da Mexico Sun Yi Kunnen-Doki A Wasan Farko

Manyan bakin da suka kalli wasan na farko sun hada da shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da shugaba Felipe Calderon na Mexico.

Karin Labarai

A cikin Wannan Email Din:

Labarai
Najeriya
Afirka
Sauran Duniya
Kiwon Lafiya

Cire Sunanka/ki

Idan an gaji da samun Kanun Labaranmu ta Email, to ana iya cire suna ko adireshi a nan Cire Sunanka/ki

Ana Bukatar Taimako?

Idan ana da wata tambaya game da Kanun Labaran nan, ana iya aika sako ga: Sashenhausa@VOANews.com

Mun sake tsarin dandalinmu domin ku samu saukin gano labarai, rahotanni, shirye-shirye, ko kuma sauti da bidiyo da hotunan da kuke bukata. Kuna iya aiko mana da ra'ayoyinku kan wannan sabon tsari namu zuwa ga: sashen-hausa@voanews.com

Cire Sunanka/ki


ليست هناك تعليقات: