الأحد، رجب ٠١، ١٤٣١

Allah ka raba mu da fitina

Manyan Labarai

'Yan Afirka Ta Kudu Su Na Murna Da Alfaharin Zuwan Gasar Cin Kofin Duniya A Kasarsu

'Yan wasan Afirka ta Kudu sun ce karawar farko da zasu yi da Mexico ita ce tamaula mafi muhimmanci da zasu taba bugawa a rayuwarsu.

Dan goyon bayan Super Eagles na Najeriya a lokacin wani wasan tayar da tsimi da kasar Koriya ta Arewa ranar lahadi.

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Ya Kafa Ma Iran Sabon Takunkumi

Wakilai 12 daga cikin 15 na Kwamitin Sulhun sun yarda da kafa sabon takunkumi a kan Iran saboda shirinta na nukiliya da ake gardama akai

Taron Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya

Attahiru Jega Shi Ne Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Najeriya

Wani babban jami'in gwamnati a Najeriya ya ce an nada Attahiru Jega a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, INEC

Attahiru Jega

Najeriya Zata Takali Muhimman Matsalolin Tattalin Arziki

Cikin abubuwan da zata takala har da batun samar da ayyukan yi da kyautata samar da rance mai sauki

Goodluck Jonathan

Isra'ila Ta Kashe Falasdinawa Hudu

Yayin da Turkiyya ke kokarin kara matsin lamba kan Isra'ila dangane da kashe 'yan rajin kare Falasdinawa 9 da ta yi a makon jiya.

Gawar Ibrahim al-Wahidi mai shekaru 25 da haihuwa, daya daga cikin wadanda Isra'ila ta kashe su na iyo cikin ruwa litinin, 7 Yuni, 2010.

Amurka Ta Kafa Takunkumi Kan Dan Tsohon Shugaba Lansana Conte Na Guinea

Ousmane Conte, dan marigayi shugaba Lansana Conte na kasar Guinea, zaune a wakafi na hedkwatar Jendarma a Conakry, babban birnin kasar, bayan da aka kama shi bisa zargin fataucin muggan kwayoyi.

'Yan Taliban Sun Kai Farmaki A Yunkurin Wargaza Taron Neman Zaman Lafiya

'Yan Taliban sanye da rigunan kunar-bakin-wake da rokoki sun kai farmaki da nufin wargaza wani taron neman zaman lafiya a Kabul

Jami'in tsaro yana gadin dan Taliban da aka kama bayan musanyar wuta laraba 2 Yuni 2010 a birnin Kabul.

Gwamnatin Najeriya Zata Kashe Daruruwan Dubban Miliyoyin Naira Don Ceto Kamfanonin JIragen Sama

Gwamnatin Najeriya ta ce zata kashe Naira miliyan dubu dari biyar don ceto kamfanonin jiragen saman kasar dake cikin kasadar wargajewa

Wani jirgin kamfanin Bellview na Najeriya yana kokarin tashi a Lagos a shekarar 2005

Hira Da Dan Wasan Kwaikwayo Mai Ban Dariya Baban Chinedu

Yusuf Haruna Funtua (Baban Chinedu)

An Amince Da Gina Masallaci A Kusa Da Inda 'Yan Ta'adda Suka Rusa Tagwayen Benaye A New York

Magoya bayan wannan shirin, cikinsu har da shugaban gundumar Manhattan sun ce yana da muhimmanci a nuna amincewa da kowane irin addini.

Karin Labarai

A cikin Wannan Email Din:

Labarai
Najeriya
Afirka
Sauran Duniya
Kiwon Lafiya

Cire Sunanka/ki

Idan an gaji da samun Kanun Labaranmu ta Email, to ana iya cire suna ko adireshi a nan Cire Sunanka/ki

Ana Bukatar Taimako?

Idan ana da wata tambaya game da Kanun Labaran nan, ana iya aika sako ga: Sashenhausa@VOANews.com

Mun sake tsarin dandalinmu domin ku samu saukin gano labarai, rahotanni, shirye-shirye, ko kuma sauti da bidiyo da hotunan da kuke bukata. Kuna iya aiko mana da ra'ayoyinku kan wannan sabon tsari namu zuwa ga: sashen-hausa@voanews.com

Cire Sunanka/ki


ليست هناك تعليقات: